Tirkashi: Saurayi ya mutu a yayin da yayi tsalle domin ya kamo wayarshi ta dubu 3 da ta fada rijiya

Tirkashi: Saurayi ya mutu a yayin da yayi tsalle domin ya kamo wayarshi ta dubu 3 da ta fada rijiya

- Tsautsayi da karar kwana ne suka ja wani mutum ya rasa ran shi a kan wayar naira dubu uku kacal

- Cisse na zaune ne a gefen rijiya amma sai cikin kuskure wayar hannun shi wacce ba ta wuce ta dubu uku ba ta fada tsundum

- Bai yi wani tunani ba kawai ya fada rijiyar don dauko wayar shi amma bai fito da rai ba sai dai dauko gawar shi aka yi

Tsautsayi da karar kwana ba a saka musu rana. Firgicin ya faru ne a titin Olanrewaju da ke Mushin a jihar Legas. Lamarin ya faru ne da yammaci a lokacin da rana tayi sanyi.

Wani mutum mai suna Cisse ya rasa ran shi bayan da ya shiga wata rijiya don samo wayar shi ta salula wacce ba ta wuce naira dubu uku ba a kasuwa.

Kamar yadda rahoton YabaLeftOnline ya bayyana, mamacin na da shago ne a yankin. Yana zaune kusa da rijiyar ne lokacin da cikin rashin sani wayar shi ta tsunduma.

Bai kakkauta ba kuwa ya daka tsalle tare da fada wa cikin rijiyar don ya dauke wayar shi. Fitowar kuwa da bai yi ta da ran shi ba kenan.

KU KARANTA: Tirkashi: Mujiya ta kai wa Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue hari a coci

Kamar yadda wani ganau ba jiyau ba mai suna Yinka ya bayyana, "masu makwabtaka da shagon shi sun fara ihun neman taimako. Hatta 'yan kwana-kwana masu kashe gobara sun zo kawo tallafi amma sai dai gawar Cisse ce ta fito daga rijiyar."

Sau da yawa magabata da malamai kan yi wa matasa ko yara nasiha da yarda da kaddara, mai kyau ko mara kyau.

A duk lokacin da bawa ya rasa wani abu na shi da yake so, akwai bukatar ya san cewa ba tare aka haife shi da wannan abun ba. Don haka zai iya rasa shi a kowanne lokaci. Abu mafi kyau shine hakuri da yadda da kaddara komai kyan ta ko muninta a rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel