Kotu ta yankewa tsohon kwamishina hukuncin shekaru 19 a gidan gyaran hali

Kotu ta yankewa tsohon kwamishina hukuncin shekaru 19 a gidan gyaran hali

- Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta (ICPC) ta gurfanar da tsohon kwamishinan aikin noma na jihar Kogi

- Babbar kotun da ke zama a Okene ta yankewa Zachaeus Atte hukuncin shekaru 19 a gidan yari a kan laifuka 8 cikin 11 da aka zargesu da shi

- Kotun ta kama tsohon kwamishinan da wasu laifuka da suka hada da rub da ciki tare da almundahar wasu kudade na manoman jihar

Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta samu damar gurfanar da Zachaeus Atte , tsohon kwamishinan aikin noma na jihar Kogi da ke Arewa ta tsakiya a Najeriya.

Kamar yadda hukumar ta sanar a wallafarta ta shafinta na tuwita, An yanke wa Atte hukunci ne sakamakon laifukan da wata babbar kotun jihar Kogi da ke zama a Okene, jihar Kogi ta kama dasu. Mai shari’a J.J Majebi ne ya jagoranci shari’ar.

An kama shi da laifuka 7 cikin 11 na wadanda ICPC ke zargin shi dasu.

DUBA WANNAN: Rashawa: Ba zan sassauta wa Abubakar ba - Gwamnan Bauchi

“An yanke masa hukuncin shekaru 19 a gidan gyaran hali sakamakon laifukan da suka hada da rub da ciki a kan kudin da za a yi amfani dasu don siyan irin kwakwar manja a raba wa manoman jihar. Wannan laifin ya ci karo da sashi na 19 na dokokin ICPC na 2000,” cewar hukumar.

“Kwamsihinan ya karba wasu kudi wadanda aka ware don sufurin irin Cocoa din da za a raba wa manoma. Wannan laifin ya ci karo da sashi na 19 na dokokin ICPC.” Hukumar ta kara da cewa.

“Kwamishinan ya halaka wasu miliyoyin kudi wadanda aka ware don siyan kayayyakin ofishin. Hakan ya ci karo da sashi na 22 sakin layi na 5 na dokokin ICPC.” In ji hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel