Harkar kiwon lafiya gwamnati na za ta fi bawa muhimmanci – Ganduje

Harkar kiwon lafiya gwamnati na za ta fi bawa muhimmanci – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jadadda kudirin gwamnatinsa na inganta harkokin lafiya da walwalar mutanen jihar musamman mata da kananan yara. Gwamnan da ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Usman Alhaji ya bayyana hakan ne yayin bude taron kungiyar.

Gwamnan ya ce, "A Kano, muna bawa mata masu ciki da kananan yara magunguna kyauta. Muna kuma da tsarin da za a mayar doka inda za a ware kashi 5 cikin dari don inganta lafiyan yara."

Ya kuma ce akwai shirin bayar da kulawa da magunguna kyauta da wadanda su kayi hatsari da wandanda ke bukatar taimakon gaggawa inda ya kara da cewa harkar lafiya ta shafi kowa saboda lafiyar yara ya danganta ne da lafiyar iyayensu.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai a bangaren kiwon lafiya kuma sun samu nasarori sosai wanda hakan ya sa aka ware makuden kudi domin yin ginegine da kafa cibiyoyin lafiya.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya da gwamnonin Kudu sun cimma matsaya kan Amotekun

Gwamnan ya kara da cewa a cikin kasafin kudin 22, gwamnatinsa ta ware kashi 15 cikin dari don fanin kiwon lafiya wanda ya dara abinda cibiyar lafiya ta duniya WHO ta bayar da shawarar a rika ware wa fanin.

Ya ce, "Gwamnatin jihar ta kammala ginin manyan asibitoci biyu da muka gada daga gwamnatocin da suka gabata a kan kudin da bai kai yadda suka ware ba, kashi 15 cikin dari na yadda suka ware a baya kuma asibitoci ne irin wadanda ake da su a kasashen duniya da suka cigaba."

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta bayar da kwangilar samar da gadajen asibiti dari hudu ga kowanne asibitoc a sabbin masarautun da aka kirkira inda ya yi alkawarin cewa za a samar da kayayyakin aiki a asibitocin da za su kula da mutanen masarautun.

Ya ce an fara aikin gina cibiyar kula da cutar daji, wadda mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya aza tubalin ginin da idan an kammala zai zama daya daga cikin mafi inganci a Afirka ta Yamma.

Ganduje ya yabawa wanda suka shirya taron a Kano inda ya yi fatan taron zai amfani mutanen Najeriya da alumma baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel