Ma’aurata sun kashe mutumin da suke zargi da kwartanci a Katsina

Ma’aurata sun kashe mutumin da suke zargi da kwartanci a Katsina

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta kama wasu ma’aurata, Badamasi Muhammad dan shekara 58 da matarsa Maimuna yar shekara 22, bisa tuhumarsa da aikata laifin kisan kai, inda ake zarginsu da kashe wani Salihu Muhammad.

Jaridar Punch ta ruwaito an gurfanar da ma’auratan ne a gaban babban kotun majistri na Katsina dake karkashin ikon Alkali mai sharia Fadila Dikko, inda Yansanda suka shaida mata cewa ma’auratan sun kashe Salihu ne a ranar 23 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Kungiyar kiristocin Najeriya ta nemi Buhari ya sallami shuwagabannin tsaron Najeriya

Malam Badamasi yana zargin Salihu da neman matarsa Maimuna ne, don haka suka gayyaceshi zuwa gidansu a wannan rana, inda shigarsa gidan keda wuya sai Badamasi ya yi amfani da kota ya buga masa a kai, nan take ya baje a kasa, duk da haka bai tsaya ba ya cigaba da dukansa.

Daga bisani jama’a suka kai masa agaji, inda suka garzaya da shi zuwa babban asibitin garin Batsari domin ceton rayuwarsa, sai dai koda aka isa asibitin likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu a sanadiyyar raunuka daya samu a kai.

Ganin haka yasa mai garin kauyen Kasai ya garzaya ofishin Yansanda dake Batsari, inda ya kai musu rahoton lamarin a ranar 24 ga watan Disamba, wannan tasa Yansanda suke tuhumar ma’auratan da laifin kisan kai kamar yadda sashi na 58 da 189 na kundin hukunta manyan laifuka ya tanada.

Daga karshe Dansanda mai shigar da kara, ASP Sani Ado ya nemi Alkalin kotun ta dage sauraron karar har sai sun kammala gudanar da cikakken bincike game da lamarin.

A yanzu haka ma’auratan wanda mazauna kauyen Kasai ne cikin karamar hukumar Batsari suna can an garkamesu a gidan gayaran halayya har zuwa ranar 20 ga watan Feburairu, kamar yadda Alkali Fadila Dikko ta bada umarni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel