Mata ta bayyana yadda Fasto ya karbi mahaifar dan da ta haifa da ya sanya har yanzu baya iya magana da tafiya

Mata ta bayyana yadda Fasto ya karbi mahaifar dan da ta haifa da ya sanya har yanzu baya iya magana da tafiya

- Wata matar aure ta bayyana halin tsaka mai wuya da faston mijinta ya jefa ta

- Ya karba mahaifar yaronta na farko wacce ya ce zai yi addu'a ne amma har yaron ya cika shekaru biyu baya iya magana ko tafiya

- Faston ya samu mijinta ya sanar dashi cewa tana da wani kwarto a makaranta wanda hakan ya hada mugun rudani da rashin zaman lafiya a gidanta

Wata matar aure ta koka da yanayin da ta ke ciki a gidan mijinta saboda damuwar da ta fada.

Ta zargi fasto da yi wa mahaifar da danta na farko ya fito ciki, wani sihiri don kuwa har yanzu da ya kai shekaru biyu ba ya iya tafiya ko magana.

Kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito, "Shekaru biyar kenan da na yi aure kuma yarana biyu. Gaskiya ina alfahari da mijina don shi ne ya sanya ni a makaranta. A halin yanzu ina shekarar karshe a jami'a. Ya kasance tamkar mahaifi gareni da yarana biyu.

KU KARANTA: Rikici ya barke yayin da miji ya fadawa matarsa cewa zai je Borno kasuwanci, ashe kishiya ya tafi ya karo mata

"Matsalar ta fara aukuwa ne lokacin da mijina ya fara sauraron wani faston shi. A haihuwata ta farko sai ya ce a ba shi mahaifar da yarona ya fito daga ciki. Haka kuwa aka yi, a cewar shi zai yi addu'a ne. Har yanzu dai yaron na nan baya tafiya ko magana duk da ya cika shekaru biyu. Ko yaushe na tuna wannan lamarin, rai na yana bani sihiri aka yi da mahaifar.

"Matsala ta biyu kuwa ita ce yadda faston nan ya ce wa mijina ina da wani kwarto a makaranta. Daga nan ne mijina ya ce sai na sanar da shi gaskiyar lamarin. Ni kuwa ban yi haka ba lokacin bani da aure,me zai sa inyi bayan nayi aure? Ya fara cewa kanwata da ke taimaka min da rainon yarana ta tafi gida. Ni kuwa na ce ba zan iya karatu da raino ba. Fatana in kammala karatuna in samu abin yi amma auren nan nawa kullum lalacewa ya ke yi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel