Ana zargin matar da ta fi arziki a Afirka da damfara

Ana zargin matar da ta fi arziki a Afirka da damfara

Lauyoyi masu bincike a kasar Angola suna zargin matar da tafi sauran mata arziki a Afirka, Isabel dos Santos da almundaha da kudi da kuma karkatar da kudade.

A cewar Attoney Janar Helder Pitta Gros, ana zargin ta da almundahana da wadaka da kudade a lokacin da ta ke shugabancin kamfanin man fetur na kasar a Sonangol.

Mr Pitta Gros ya shaidawa manema labarai a yammacin ranar Laraba cewa: "Ana zargin Isabela dos Santos da almundaha da wadaka da kudade a lokacin wa'adin ta na karshe a Sonangol hakan yaza ake tuhumar ta da laifin karkatar da kudade, aikata ba dai-dai ba ... wallafa takardun bogi da wasu laifuka da suka shafi kudi."

Takardun da aka fitar a makon nan ya nuna cewa diyar tsohon shugaban kasar Jose Eduardo dos Santos da ake yi wa lakabi da matar da ta fi sauran mata kudi a Afirka da yanzu ta ke zaune a kasar Ingila ta karkatar da kudi kimanin dalar Amurka biliyan 2.1 don gina kasuwancin ta.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya da gwamnonin Kudu sun cimma matsaya kan Amotekun

Ana zargin Isabel dos Santos da amfani da amfani da matsayinta na diyar tsohon shugaban kasa inda ta handame kudaden kasar ta kai su kasashen ketare da taimakon wasu kamfanonin kasashen ketare.

Isabela tayi kaura daga kasar Angola bayan mahaifinta ya sauka daga mulki a 2017 bayan kwashe shekaru arbain yana mulkar kasar kuma ya zabi wanda yake son ya gaje shi Joa Lourenco.

A halin yanzu dai Isabela ta musanta dukkan zargin da ake mata na rashawa bayan fitowar takardun, ta kuma shaidawa BBC cewa akwai yiwuwar ta tsaya takarar shugabancin kasa a Angola.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel