Da duminsa: An bayyana ranar kaddamar da sabbin jiragen yakin da Najeriya ta saya (Hotuna)

Da duminsa: An bayyana ranar kaddamar da sabbin jiragen yakin da Najeriya ta saya (Hotuna)

Hukumar mayakan saman Najeriya ta bayyana ranar da za'a kaddamar da sabbin jirage masu saukar angulu biyu da gwamnatin tarayya ta saya domin yakan yan ta'adda.

Kakakin hukumar, Ibikunle Daramola, ya bayyana hakan da daren Alhamis bayan babban hafsan hukumar, CAS Sadique Baba Abubakar, ya fita yawon duba sabbin jiragen.

Ya bayyana cewa Shugaba Buhari zai kaddamar da su ranar Talata. 28 ga watan Junairu, 2020 a Abuja.

Yace: "A yau, AM Sadique ya duba sabbin jirage masu saukar angulu kirar AGUSTA 109 da muka saya bayan an kammala hadasu a cibiyar 307 Executive Airlift Group."

"A yanzu komai a shirye yake domin kaddamar da jiragen da shugaba Muhammadu Buhari zai yi ranar 28 ga watan Jumairu, 2020 a farfajiyar Eagle Square dake Abuja."

Da duminsa: An bayyana ranar kaddamar da sabbin jiragen yakin da Najeriya ta saya (Hotuna)
Jirgin
Asali: Facebook

DUBA NAN Cikin shekaru 3, Gwamnatin Buhari ta kashe N1.7tr kan wutan lantarki - El-Rufa'i

Da duminsa: An bayyana ranar kaddamar da sabbin jiragen yakin da Najeriya ta saya (Hotuna)
CAS Baba

Mun kawo muku a bayan cewa AM Sadique ya ce hukumar ta sayi jirage masu saukan angulu biyu domin yakan yan ta'adda da yan bindiga a yankin Arewa maso yamma.

"Wasu Makaman (da akayi oda) sun fara isowa. A wajen mayakan sama, jiragen yaki masu saukar angulu biyu sun iso ranar 15 ga Junairu kuma muna kan shiryasu yanzu." A cewarsa

Najeriya na fama da rashin tsaro a kusan dukkan sassan jihar. Wadannan sun hada da Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabas, yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Arewa maso yamma da kuma yan bindiga makiyaya a kudu maso yamma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel