IPPIS: FG ta dakatar da albashin mambobin ASUU da ASUP

IPPIS: FG ta dakatar da albashin mambobin ASUU da ASUP

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin dakatar da albashin duk malaman jami'ar da suka ki yin rijitsa da Integrated Personnel and Payroll Information System (IPPIS) da gaggawa.

Malaman da abin ya shafa ba za a biya su albashin watan Janairu ba kuma sun hada da malamai massu koyarwa a jami'o'i, kwalejojin ilimi da foliteknik.

Ofishin babba akanta na kasa ya mika wasikar da daraktan IPPIS, Olufehinti O. J yasa hannu kuma mai kwanan wata 21 ga watan Janairu 2020 ga dukkan manyan makarantun a kan kada su saki albashin watan Janairu ga wadanda basu yi rijista ba.

kamar yadda wasikar ta bayyan, "An umarce ni da in sanar da ku cewa ana kan shirya albashin watan Janairu 2020 kuma za a kammala nan da ranar 29 ga watan janairu 202. A don haka ne aka umarci dukkan ma'aikatu, bangarori da cibiyoyi da su tabbatar da ma'aikatansu na kan tsarin IPPIS.

DUBA WANNAN: Kungiyar Shi'a tayi magana a kan jita-jitar mutuwar Zakzaky

"Don tabbatar da wannan tsarin, ana umartarku da kada ku saki albashin manyan makarantun da basu yi rijista ba don albashin watan janairu za a biya shi ne a kan tsarin IPPIS."

Idan zamu tuna, kungiyar malaman jami'o'in ta jaddada cewa mambobinta ba zasu shiga tsarin IPPIS ba.

Mambobin kungiyar sun ki yin rijista da tsarin a lokacin da jami'ai daga ofishin babban akantan kasar nan suka ziyarci makarantun don yi wa malam rijista.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel