Amotekun: An yiwa furucina bahaguwar fahimta ne - Malami

Amotekun: An yiwa furucina bahaguwar fahimta ne - Malami

- Abubakar Malami (SAN) a ranar Alhamis, 23 ga watan Janairu ya soke furucinsa na farko game da billowar kayan tsaro na kudancin Najeriya wanda ya ce ba ya bisa oka

- Malami ya yi ikirarin cewa gwamnonin kudu maso yamma da mutanen kudancin Najeriya be suka yiwa kalamin nasa wata fassara na daban

- Ya bayyana hakan ne a hira da gidan radiyo na Najeriya a Abuja

Atoni janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN) a ranar Alhamis, 23 ga watan Janairu ya soke furucinsa na farko game da billowar kayan tsaro na kudancin Najeriya wanda ya kaddamar a matsayin ba bisa ka’ida ba.

Malami wanda sukar kayan Operation Amotekun da ya yi ya haifar da cece-kuce a shafukan sadarwa ya yi ikirarin cewa gwamnonin kudu maso yamma da mutanen kudancin Najeriya be suka yiwa kalamin nasa wata fassara na daban.

KU KARANTA KUMA: Abdulmumin Jibrin ya saduda, yana neman sulhu da shugabannin APC gabannin zaben da za a sake (bidiyo)

Atoni Janar din wanda ya yi wannan jawabin a wata hira da gidan radiyo na Najeriya a Abuja a safiya yau Alhamis ya ce “an yiwa furucina kan Operation Amotekun wata fassara ne na daban, ban ce baya bisa doka ba.”

A baya mun ji cewa Sakataren kungiyar Afenifere na kasa, Kole Omololu, ya caccaki jagaban Bola Tinubu a kan matsayarsa a sabon salon tsaro da aka kirkiro a yankin Kudu maso yamma mai suna Amotekun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel