Rashawa: Ba zan sassauta wa Abubakar ba - Gwamnan Bauchi

Rashawa: Ba zan sassauta wa Abubakar ba - Gwamnan Bauchi

- Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya ce ba zai raga wa magabacinsa Mohammed Abubakar ba muddin ya same shi da laifin rashawa

- Gwamna Mohammed ya yi wannan jawabin ne bayan da kotun koli a Abuja ta tabbatar da shi a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar

- Bala Mohammed ya ce ba zai bar duk wani da aka samu da hannu wurin cin amanar gwamnatin Bauchi da mutanen jihar ba

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ce ba zai sassauta wa magabacinsa, Alhaji Mohammed Abubakar ba idan ya same shi da laifin almundaha da dukiyar mutanen jihar yayin da ya ke mulki.

The Punch ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyi da manema labarai na gidan gwamnati su kayi masa jim kadan bayan dawowansa daga Abuja inda kotun koli ta tabbatar da shi a matsayin zababen gwamnan jihar.

Ya ce, "Ni mutum ne mai kawaici amma a bangaren shugabanci duk inda na gano cewa an cuci gwamnati ko mutanen Bauchi ba zan kyalle shi ba saboda babu wanda ya sassauta min lokacin da na sauka daga mulki a Abuja. Babu wanda aka taba bincika a kasar nan kaman ni kuma ina kallubalantarsu su zo su nuna inda na kwashe kudi na boye."

DUBA WANNAN: Sokoto: Hukuncin kotun koli ba zai rage mu da komai ba - Wamakko

Tsohon minitsan na Abuja ya ce karar da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta suka shigar na kallubalantar nasararsa ba komai bane illa bata lokaci.

"Shari'ar da aka gudanar a kotun duk bata lokaci ne, a gani na babu bukatan shigar da karar. Ba zan iya hambarar da shi ba idan ba ikon Allah da kuma kuri'un da mutan Bauchi suka bani ba. Abin ya min ciwo don bani da kudin da zan kashe a kotu. Sai dai duk da hakan a shirye na ke in yafe don haka demokradiyya ta gada."

Ya yi alkawarin gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar nan da watanni shida masu zuwa bayan an kwashe shekaru 13 a jihar ba tare da yin zaben kananan hukumomi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel