Najeriya ce kasa mafi fama da rashawa ta 4 a Afrika ta yamma - Binciken TI

Najeriya ce kasa mafi fama da rashawa ta 4 a Afrika ta yamma - Binciken TI

Najeriya ta zo kasa ta hudu a yammacin nahiyar Afrika mafi fama da cin hanci da rashawa a sabon rahoton binciken da kungiyar Transparency International ta saki na shekarar 2019.

A wannan karon, Najeriya ta biyo bayan kasar Kamaru, Chadi, Libiya da Equatorial Guinea

Rahoton TI ya nuna cewa cin hanci da rashawa na kara yawa a kasashen yammacin Afrika musamman lokukan zabe wajen saye kuri'u.

A rahoton wannan shekarar, Najeriya ta samu maki daya da kasashe irinsu Iran, Honduras, Guatemala, Bangladesh, Mozambique da Angola.

Cikin kasashe 180 da aka gudanar da bincike kansu, Najeriya ce ta zo na 152. Hakan na nufin cewa kasashe 28 kadai sukafi Najeriya rashawa a duniya.

Kasashen sune - Comoros, Cameroon, Central African Republic, Uzbekistan, Tajikistan, Madagascar, Zimbabwe, Eritrea, Nicaragua, Cambodia, Chad, Iraq, Burundi, Congo, Turkmenistan, Haiti, Democratic Republic of Congo, Libya, Guinea-Bissau, North Korea, Venezuela, Equatorial Guinea, Sudan, Afghanistan, Yemen, Syria, South Sudan and Somalia.

Kasashen da suke da mafi karancin rashawa sune New Zealand, Denmark, Finland (86), Switzerland (85), Singapore (85), Sweden (85), Norway (84), Netherlands (82), Luxembourg (80) da Jamus(80).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel