Hanyar Kaduna - Zariya: An dakile masu garkuwa da mutane, an kashe 2, an ceto mutane 11

Hanyar Kaduna - Zariya: An dakile masu garkuwa da mutane, an kashe 2, an ceto mutane 11

Hukumar yan sandan jihar Kaduna a daren Laraba ta bayyana cewa ta samu nasarar dakile wasu masu garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Zariya inda aka hallaka biyu kuma aka ceto mutane 11

Wannan na faruwa ne mako daya bayan harin da aka kaiwa sarkin Potiskum da wani kwamandan Soji a hanyar.

Hakazalika jami'an yan sandan sun ceto wasu mutane 9 da aka yi awon gaba da su a cikin mota kirar Marcopolo a hanyar, a jawabin da kakakin hukumar, DSP Yakubu Sabo, ya saki a daren Laraba.

Yace: "Hukumar yan sanda na jihar Kaduna ta samu nasarar dakile yunkurin garkuwa da wasu mutane inda ta bindige yan bindigan biyu kuma aka ceto mutane 11."

"A ranar 22/1/2020 misalin karfe 12:30 na dare, hukumar ta samu labarin wayar tarho ta DPO na Mararaban Jos cewa wasu yan bindiga sun tare hanyar Kaduna zuwa Zariya kuma sun sace matafiyan Abuja zuwa Kano 8 a wata motar Sharon masu suna; Aisha Umar, Samira Ibrahim Dakata, Safiya Idris, Hauwa Aliyu, Aisha Yakubu, Ma’aru Adam, Safiya Audu and Yahaya Bello."

"Da muka samun labarin, hukumar ta tura jami'ai wajen inda suka batakashi da yan bindigan, aka kashe biyu cikinsu kuma aka ceto mutane takwas yayinda sauran yan bindigan suka arce da raunuka."

"A wani harin kuma da ya faru ranar 21/1/2020 misalin karfe 6 na yamma, hukumar ta samu rahoto daga mutan gari ta bakin DPO na Kidandan a karamar hukumar Giwa inda wasu yan bindiga suka far wa kauyen Maidaro kuma suka sace ma'aikatan kamfanin sadarwan Airtel uku."

"Da wuri aka tura jami'ai inda suka yi musayar wuta da yan bindigan kuma suka samu nasarar ceto ma'aikatan uku masu suna, Henry Agim, Kamal Raman da Shegun Adejimoh.

"Yayinda muke kokarin binciko yan bindigan da suka gudu, jami'anmu sun yi arangama da wasu mutane 9 da aka sace a motar Macorpolo da aka kaiwa hari ranar 14/01/2020 tare da sarkin Potiskum."

"Sun bayyana sunayensu matsayin Abdulhafiz Wakil, Abdul Wasiu Jimoh, Mujittaba, Hajara Usman, Emmanuela Dimka, Dahiru Isa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel