Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 55

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 55

- Wani matashi mai shekaru 20 ya shiga hannun 'yan sanda bayan da ya kashe mahaifiyar shi har lahira

- An gano cewa matashin ya buga wa mahaifiyar shi tukunyar girki ne a kai sau da yawa wanda hakan ya kawo mata ajali

- Tuni matasan yankin suka bi shi har daji inda ya buya tare da mika shi ga 'yan sanda don a hukunta shi

'Yan sanda sun kama wani matashi mai shekaru 20 a Aboabo da ke yankin Tamale na yankin Arewaci sakamakon zargin shi da suke da kashe mahaifiyar shi mai shekaru 55 a gidanta.

Osman Abdul Moomen ya kashe mahaifiyar shi ne a safiyar ranar Talata da wajen karfe 10:30 kuma ya gudu don samun wajen buya a wani daji mafi kusa.

An samu mahaifiyar dauke da raunika masu tsanani wanda aka ji mata da tukunyar abinci. An gano cewa ya buga mata tukunyar ne sau ba adadi a kanta wanda hakan ya kawo ajali, kamar yadda jaridar Ghana web ta ruwaito.

Har yanzu dai ba a san abinda ya hada fadan tsakanin mahaifiyar da yaron ba.

KU KARANTA: Kamar karya: Maza kala-kala matata ke kaiwa gadonmu na sunnah - Miji ya koka

Matasan yankin ne suka bazama neman Moomen wanda suka samu a daji kuma suka mika shi ga 'yan sanda.

Babban jami'in 'yan sandan yankin Tamale, DSO Mick Omari Boakye ya ce an kira 'yan sandan ne bayan aukuwar lamarin. Amma matasan yankin sun ki barin a dauke gawar zuwa asibitin koyarwa na Tamale don duba musabbabin mutuwar.

Kamar yadda ASP Omari Boakye ya sanar, yankin na musulmai ne wadanda basu amincewa gawa ta dade ba tare da an birneta ba.

"Mun yi magana da su amma sun hana mu duba gawar," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng