Sokoto: Hukuncin kotun koli ba zai rage mu da komai ba - Wamakko

Sokoto: Hukuncin kotun koli ba zai rage mu da komai ba - Wamakko

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a jiya Alhamis ya ce hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaben gwamna na jihar Sokoto ba zai rage wa jam'iyyar All Progressives Congress APC magoya baya a jihar ba.

Hukuncin kotun ya tabbatar da nasarar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal kuma ta yi watsi da daukaka karar da jam'iyyar APC da dan takararta Ahmad Aliyu suka shigar.

Ganin irin dandazon magoya bayan jam'iyyar APC da suka tarbi shi da ministan harkokin yan sanda a filin tashi da saukan jirage na Sultan Abubakar III, tsohon gwamnan jihar ya rungumi kaddara inda ya ce hukuncin kotun kaddara ce daga Allah.

Ya ce sun rungumi kaddara duk da cewa hukuncin kotun kolin ya basu mamaki duba da irin hujojji da suka gabatarwa kotun.

Wamakko wanda ya shafe sa'o'i kafin isa gidarsa da bai wuce tafiyan mintuna 15 ba daga filin tashin jiragen saman ya mika godiyarsa ga Allah. Ya bukaci magoya bayan jam'iyyar APC su cigaba da kasancewa masu biyayya da doka.

DUBA WANNAN: Kano: Dattijan APC sun bayyana matsayarsu a kan zaben maimaici na Kiru/Bebeji

Ya bukaci su fito kwansu da kwarkwata du zabi yan takararsu a zaben da za a maimaita a ranar Asabar a jihar.

Ya ce, "APC jam'iyya ce mai son zaman lafiya kuma magoya bayan ta masu biyaya ga dola ne. Ba mu zagezage ko furta kalaman tayar da hankula. Saboda haka ina kira gare ku ku cigaba da zama lafiya kuyi aiki don jamiyyar ta yi nasara."

A jawabinsa, Ministan harkokin yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ya ce ya yi mamakin jin hukuncin da kotun ta yanke amma sun bar wa Allah komai.

Dan takarar gwamnan jam'iyyar a zaben da ta gabata, Ahmad Aliyu ya ce hukuncin kotun ya sake kusantar da su ga mutanen jihar da ke neman ganin canji cikin gaggawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel