Yau a tarihi: Hadarin jirgin da yayi sanadiyar mutuwar mahajjata kimanin 180 a Kano a 1973

Yau a tarihi: Hadarin jirgin da yayi sanadiyar mutuwar mahajjata kimanin 180 a Kano a 1973

A 1973, wani jirgin sama dauke da Alhazan da suka kammala aikin Ibadar Hajji da kasa mai sarki ya samu hadari yayinda yake kokarin sauka a babban filin jirgin saman Malam Aminu Kano inda ake tsoron mutane 180 sun rigamu gidan gaskiya.

Mutane 22 sun tsallake rijiya da baya; wannan ya hada da matukin jirgin da ma'aikatan jirgin, bisa ga rahoton New York Times.

Wannan shine hadarin jirgi mafi tayar da hankali zuwa lokacin. Gabanin 1973, jirgin kasar Rasha ne ya taba hadari inda mutane 176 suka hallaka.

Jirgin mahajjatan mai kirar Boeing 707, mallakan kasar Jordan na daya daga cikin jiragen da ke jigilar mahajjatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya a lokacin.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya kama da wuta ne yayinda ya nufi filin jirgin saman Kano. Amma dai ba'a tabbata ko jirgin ya taba kasa ba a lokacin.

Allah ya jikansu da rahama, ya karbi ibadarsu kuma ya kyautata makwancinsu.

A bangare guda, Cikin kuskure Kasar Iran ta baro jirgin saman Ukraniyar da yayi hadari ranar Laraba, inda dukkan mutanen ciki 176 gaba daya suka hallaka, jami'an kasar Amurka sun tabbatar.

Jirgin ya yi hadari ne bayan tashi daga filin jirgin saman Tehran.

Wannan hadari ya faru ne bayan kasar Iran ta kai hari sansanin Sojin Amurka biyu a kasar Iraqi.

Tashar CBS ta ruwaito cewa hukumomin leken asirin kasar Amurka sun yi ikirarin cewa sun ga rokoki masu inzami biyu gab da jirgin ya kama da wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel