'Yan bindiga sun kashe wani jigon APC a Ibadan

'Yan bindiga sun kashe wani jigon APC a Ibadan

Wasu wadanda ake zargin makasan haya ne sun harbe wani jigon jam’iyyar APC a ranar Laraba a jihar Oyo. Makasan da ake zargin na haya ne sun harbe Babatunde Oreitan ne da rana a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Oreitan na daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC a karamar hukumar Ona Ara da ke jihar Oyo.

Majiyoyi masu yawa sun tabbatar da cewa na kashe jigon jam’iyyar ne a gidansa da ke a yankin Oremeji Agugu na jihar.

Jaridar Premium Times ta gano cewa an kashe shi ne bayan sallar azahar a masallacin da ke gidansa, duk da har yanzu ba a samu cikakken bayani a kan hakan ba.

An kasa samun Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi, a wayar tafi da gidanka kuma bai mayar da martanin sakonnin da aka dinga tura masa ba.

DUBA WANNAN: An damke wani kwarto da ke sanya kayan mata yana zuwa gidan matan aure suna zina (Hotuna)

Amma kuma mataimakin shugaban matasan jam’iyyar APC, Afeez Mobolaji ya tabbatar da kisan.

Mobolaji, tsohon mai bada shawara ta musamman ne ga tsohon gwamnan jihar, Abiola Ajimobi, a kan harkokin matasa da dalibai. Ya kwatanta rashin da babban rashi ga Musulunci.

Ya ce, “Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ona Ara, Alhaji babatunde Oreitan ya rasu a yau Laraba kuma wasu da ake zargin makasan haya ne suka halaka shi. Babatunde musulmi ne na gari kuma dan siyasa ne mai ra’ayin kansa. Wadanda suka kashe shi ba zasu taba samun natsuwa ba. Muna fatan Ubangiji ya yi masa rahama.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel