Yanzu-yanzu: Shugaban masu garkuwa da mutane na Abuja da 'yan kungiyarsa 36 sun mika kansu ga hukuma

Yanzu-yanzu: Shugaban masu garkuwa da mutane na Abuja da 'yan kungiyarsa 36 sun mika kansu ga hukuma

- Buju Bazamfare, gawurtaccen mai garkuwa da mutane da 'yan kungiyarsa 36 sun ajiye makamai sun mika kansu ga 'yan sanda

- Bazamfare da 'yan kungiyarsa sun dade suna adabar matafiya da kuma mutanen jihohin Nasarawa, Kogi da birnin tarayya, Abuja

- Mai martaba sarkin Keffi, Dr Shehu Chindo Yamusa yana daga cikin wadanda suka taka muhimmiyar rawa don ganin Bazamfare ya mika kansa

Shugaban masu garkuwa da mutane, Buju Bazamfare tare da 'yan kungiyarsa 36 da suka dade suna addabar matafiya da mazauna babban birnin tarayya, Abuja, Nasarawa da Kogi sun mika kansu ga rundunar 'yan sandan Najeriya a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa a ranar Laraba.

Ana zargin shi da 'yan kungiyarsa ne suka adabar mutanen kananan hukumomin Toto da Nasarawa da kuma Abaji da Kuje a Abuja da Bassa da Lokoja a jihar Kogi.

Daily Trust ta gano cewa Sarkin Keffi, Dr Shehu Chindo Yamusa ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin Bazamfare da 'yan kungiyarsa sun ajiye makamai sun rungumi zaman lafiya.

DUBA WANNAN: Shugaban PDP na Kano, Rabiu Bichi ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya ya koma APC

A baya, mun ruwaito muku cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane da ke jihar, Buju Bazamfare ya mika kai kuma ya ajiye makamansa.

Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar godiya da ya kai wa Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu a Abuja a ranar Alhamis.

Gwamnan ya yabawa 'yan sanda a jihar, musamman kwamishinan 'yan sanda, Bola Longe da tawagarsa saboda tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar, inda ya fadawa IGP din cewa ya yi ido biyu da mai garkuwa da mutanen da wasu da suka amince su ajiye makamansu.

Gwamnan ya shaidawa IGP cewa, "An fada min yayin taron cewa sun amince za su gana da kai ido da ido kuma su mika maka makamansu tare da mika kansu."

Gwamnan ya ce wannan babban nasara ce a jihar a kokarin da ta ke yi na rage laifuka kuma ya godewa IGP kan gudunmawar da ya ke baiwa jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel