Yadda Sojoji suka budewa yan sandan da suka dakile wasu yan Boko Haram wuta

Yadda Sojoji suka budewa yan sandan da suka dakile wasu yan Boko Haram wuta

An shiga rudani a garin Mainok, dake babban hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a jihar Borno, bayan wasu Sojoji sun budewa jami'an yan sandan SARS da sukayi artabu da sukayi da yan Boko Haram. Cewar TheCable

Ofishin SARS sashe ne na hukumar yan sandan Najeriya da suka shahara da yakan yan fashi da makami.

Kauyukan da ke tsakanin Borno da Yobe na fuskantar barazana daga hannun yan Boko Haram tun da aka shiga sabuwar shekara.

A ranar Litnin da suka sake kawo hari Mainok, an ce Sojoji da yan garin sun arce, hakan ya baiwa yan ta'addan daman cin karansu ba babbaka.

Amma jami'an yan sandan SARS da RRS suka dumfari yan ta'addan kuma suka kawar da su, cewar wani mazaunin Mainok.

Daya daga cikin jami'an SARS din da suka fitittiki yan Boko Haram ya bayyanawa manema labarai cewa bayan dakile yan ta'addan kuma suna kokarin fitowa, sai Sojoji suka bude musu wuta.

Jami'in dan sandan wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya ce abin ya basu mamaki da suka ga Sojoji ke harbinsu.

Yace: "An tura mu Mainok bayan samun labarin cewa yan Boko Haram sun kai hari. Da muka isa wajen, mun tarar yan Boko Haram sun kashe mutane kuma sun lalata gidajensu."

"Sai muka bude musu wuta na tsawon kimanin awa daya. Mun samu galaba a kansu kuma mun kwace motocinsu biyu Hilux da makamai. Abin mamakin shine yayinda muke kokarin fitowa, wasu Sojoji suka kawo mana hari."

"Sun har-harba mana rokoki har daya daga cikin motoci maras jin bindiga da sifeto janar ya bamu ya lalace."

Yace amma kwamandansu ya umurcesu kada su harbi Sojojin har sai lokacin da wasu Sojoji suka zo daga Benisheik suka tsagaita wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel