An kama wani mutum ya boye kayan sata a cikin wandonsa a wani shago a Abuja (Hotuna)

An kama wani mutum ya boye kayan sata a cikin wandonsa a wani shago a Abuja (Hotuna)

An kama wani mutum sanye da kaya na kammala ya saci kaya daga wannan babban kantin sayar da tufafi a Abuja ya boye su cikin gajeren wandonsa.

Yayin da wasu ke aiki tukuru don ganin sun nemi na kansu, wasu kuma sun gwammace su nemi hanyar gaggawa ba ta halas ba sai dai galibi hakan na zama musu fitina.

Kamar dai wannan mutumin da na'urar daukan bidiyon sirri ta CCTV ta hasko shi yana satar kaya a wani kanti a Abuja yana boye wa cikin gajeren wandonsa.

Mutumin ya sace kayan ne bayan yarinyar da ke sayar da a shagon da ke Gwarimpa ta tafi sanar da shugabanta farashin da mutumin ya taya wani tufafi da ya ke son saya.

Hotunan da aka wallafa sun nuna cewa an kama mutumin kuma an kunyatta shi a wajen kantin.

DUBA WANNAN: An damke wani kwarto da ke sanya kayan mata yana zuwa gidan matan aure suna zina (Hotuna)

Wani mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook, Gwen Divy Ifeson ya wallafa hotunan mutumin inda ya rubuta cewa: "Ya tafi kantin sayar da tufafi, ya taya kaya ya kuma bukaci yarinyan shagon ta tafi ta kira mai gidanta don su karkare cinikin. Da fitar yarinyan sai ya sace wasu kaya ya boye cikin gajeren wandonsa ya kama hanya zai fita.

"Amma bai san cewa mai shagon yana kallonsa ba a na'urar bidiyo ta CCTV."

Sai dai daga bisani asirinsa ya tonu kuma an gano abinda ya aikata.

Bisa ga dukkan alamu dai za a mika shi hannun hukuma ne domin su dauki matakin da ya dace a kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel