Yan Boko Haram sun yi niyyar sakin Rabaran Andimi amma daga baya suka kasheshi - Buhari

Yan Boko Haram sun yi niyyar sakin Rabaran Andimi amma daga baya suka kasheshi - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya CAN na karamar hukumar Michika a jihar Adamawa, Lawan Andimi.

Buhari ya siffanta kisan matsayin abin takaici da rashin imani.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Talata a Abuja.

Yace: "Yan ta'addan sun kashe Malamin addinin yayinda suke nuna niyyar sakeshi ta hannun wasu."

Shugaban kasan ya jajantawa al'ummar Kirista a fadin Najeriya, gwamnati da al'ummar jihar Adamawa bisa ga rashin malaminsu.

DUBA NAN Akalla Sojoji 17 sun hallaka, an yi awon gaba da mutane da dama a sabon harin Boko Haram

Shugaban kungiyar CAN, shiyar jihar Adamawa, Dami Mamza, ya bayyana kudin fansan da yan Boko Haram suka bukata kafin kashe Rabaran Lawan Andimi a ranar Litnin.

A cewar Dami Mamza, yan ta'addan sun bukaci N800m kafin sun sake Lawan Andimi.

Yayinda yake hira da TheCable ranar Talata Mamza ya ce kungiyar ba ta da irin wannan kudin da yan ta'addan ke bukata.

A Ranar Alhamis, 2 ga Watan Junairu, 2019, ‘Yan Boko Haram sun kai hari, inda su ka sace babban Faston da ke Kauyen na Michika.

Bayan yan kwanaki, Boko Haram ta saki bidiyo inda Faston ke rokon gwamnan jihar Adamawa, Adamu Fintiri da kungiyar CAN su ceceshi daga hannun yan ta'addan.

Tun daga lokacin ba'a sake ji daga gareshi ba sia dai labarin mutuwarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel