An damke wani kwarto da ke sanya kayan mata yana zuwa gidan matan aure suna zina (Hotuna)

An damke wani kwarto da ke sanya kayan mata yana zuwa gidan matan aure suna zina (Hotuna)

Wani mai amfani da dandalin sada zumunta na Facebook da ke zaune a Benin City, Felix Eigbefo ya wallafa hotunan wani mutum da ya yi bada kama cikin wani tufafi mai kama da lulubi na mata domin ya shiga gidan mata su aikata zina.

Da ya ke wallafa hotunan mutumin bayan an damke shi, Felix ya rubuta:

"Namiji ya yi shigan mata domin ya samu damar aikata zina da mace a gidan mijinta kan shimfidan aurenta.

"Sai dai asirinsa ya tonu!

Ni: Rayuwa kenan"

Rahotanni sun bayyana cewa makwabta sun bayyana cewa sun dade suna ganinsa yana shiga gidan sanye da irin wannan tufafin kuma sun zargin ba dai-dai ba sai dai suka yi gum da bakinsu suna tunanin kila kawarta ce sai da dubunsu ya cika mijin ya kama shi.

Mutumin ya saba zuwa ya shiga dakin matan a duk lokacin da mijin baya gidan a cewar rahoton.

Ga dai hotunan mutumin yayin da aka kama shi:

An damke wani kwarto da ke sanya kayan mata yana zuwa gidan matan aure suna zina
An damke wani kwarto da ke sanya kayan mata yana zuwa gidan matan aure suna zina
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yadda matar aure da umurci mijinta ya rika kwanciya da mahaifyarta saboda neman abin duniya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel