N800m Boko Haram ta bukata kudin fansa shugabanmu - Kungiyar CAN

N800m Boko Haram ta bukata kudin fansa shugabanmu - Kungiyar CAN

Shugaban kungiyar mabiya addinin Kirista a Najeriya, shiyar jihar Adamawa, Dami Mamza, ya bayyana kudin fansan da yan Boko Haram suka bukata kafin kashe Rabaran Lawan Andimi a ranar Litnin.

A cewar Dami Mamza, yan ta'addan sun bukaci N800m kafin sun sake Lawan Andimi.

Yayinda yake hira da TheCable ranar Talata Mamza ya ce kungiyar ba ta irin wannan kudin da yan ta'addan ke bukata.

Yace: "Sun bukaci €2 million (N800m). Bamu da irin wannan kudin nan. Amma ba don hakan suka kasheshi ba. Na tabbata sun yanke shawarar kashe shi. Shirinsu kenan kuma babu abinda zamuyi domin hanasu."

"Sun tuntubi kungiya kuma mun tattauna. Daga baya kuma suka sharemu suka kashe shi."

Mun kawo muku rahoton cewa Yan kungiyar tada kayar bayar Boko Haram sun hallaka, Rabaran Lawal Andimi, shugaban kungiyar kiristocin Najeriya CAN a karamar hukumar Michika, jihar Adamawa.

Yan ta'addan sun yi awon gaba da Lawal Andimi ne a farkon watan a kauyensa.

Dan jarida, Ahmad Salkida, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita da safiyar yau Talata, 21 ga watan Junairu, 2020.

A Ranar Alhamis, 2 ga Watan Junairu, 2019, ‘Yan Boko Haram sun kai hari, har su ka sace babban Faston da ke Kauyen na Michika.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel