Buhari ya sabunta nadin mutane 2 dake bashi shawara a kan lamuran gajiyayyu

Buhari ya sabunta nadin mutane 2 dake bashi shawara a kan lamuran gajiyayyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Samuel Ankeli a matsayin babban mataimaki na musamman (SSA) a kan lamuran gajiyayyu.

Ya kara nada Malam Garba Shehu a matsayin mataimaki na musamman (SA) a kan lamurra gajiyayyu.

Nadin ya fara aiki ne daga ranar 15 ga watan Oktoba 2019, kamar yadda takardar da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaba Buhari a kan yada labarai ya fitar.

An fara nada hadiman na musamman din ne tun lokacin da shugaban kasar ya fara hawa mulkin kasar a karo na farko.

A wani labari na daban, Makaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa hukumarsa zata nemi a dawo da duk wasu mabarbata dukiyar jama'ar Najeriya da suka turai suka buya.

DUBA WANNAN: Zamu dawo da duk mabarnatan da suka gudu turai suka buya - Magu

Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da yake gana wa da manema labarai a ofishin shiyyar hukumar na Ilorin.

Magu, wanda ya kai ziyarar aiki jihar Kwara, ya bayyana cewa an shigo sabuwar shekara, a saboda haka hukumar EFCC ta sabunta yakin da take yi da karya tattalin arziki kuma za a gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

"Zamu gayyaci da duk wanda muke bincike, sannan mu gurfanar da shi a gaban kotu da zarar mun kammala bincike. Wannan somin tabi ne, zamu nemi a dawo da mabarnata da dama da suka gudu turai suka buya, basu tsira ba don kawai suna zaune a kasashen ketare. Tamkar yanzu muka fara yaki da cin hanci, mun fito da karfinmu a sabuwar shekaru," a cewar Magu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel