EFCC na son firgita ni - Saraki

EFCC na son firgita ni - Saraki

- Tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki ya zargi hukumar yaki da rashawa ta EFCC da yunkurin firgita shi

- Saraki ya sanar da hakan ne a karar da ya kai hukumar a kan kwace masa gidajensa da aka yi na Ilorin

- Tsohon shugaban majalisar dattijan ya zargi EFCC din da tsallake umarnin kotun kolin Najeriya ta hanyar samun yarjewar wata kotu kasa da ita

Tsohon shugaban majalisar dattijan Najeriya ya zargi hukumar yaki da rashawa ta EFCC da yunkurin dimauta shi ta hanyar kwace gidajensa da ke Ilorin. Saraki ya yi wannan zargin ne a ranar Talata, 21 ga watan Janairu a yayin da wata babbar kotun tarayya ke sauraron karar da ya kai ta EFCC din a kan kwace masa gidajensa da ke Ilorin, Jaraidar The Nation ta ruwaito.

Ya kwatanta sabuwar karar da EFCC din ta shigar da amfani da kotu ba ta yadda ya dace ba. Ya ce kotun ta kara duba hukuncin da kotun koli ta yanke na wankesa.

Dan siyasar ya sanar da cewa kotun koli ta wanke sa tsaf a kan zargin kudaden da kuma gidajen nasa kuma ta bukaci duk wata kotu da tayi watsi da wannan koken.

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon Alƙalin kotun kolin Najeriya rasuwa Read more:

Mai shari'a Aikawa ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 5 ga watan Fabrairu don duba koken da Saraki ya bayyana.

Idan zamu tuna, a kwanakin baya ne hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kwace wasu gidajen tsohon shugaban majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki.

A kuma cikin kwanakin ne gwamnatin jihar Kwara ta murkushe gidansu wanda yayi ikirarin na gado ne. Hakan kuwa ya fusata tsohon shugaban majalisar wanda har ministar Buhari, Gbemisola Saraki sai da ta saka baki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel