Mun shafe shekaru ina kwanciya da Fasto din cocin mu a kan gadon auren mu - Matar aure na neman shawara
- Wata mata mai suna Adedolapo ta koka da yadda mijinta ya zama tamkar mijin mahaifinta
- Wata matar aure da ta boye sunanta ta bukaci shawarar mutane a kan cin amanar mijinta da take yi da fasto
- Ta bayyana cewa kiyayya mai tsanani ta fara shiga tsakaninta da mijinta wanda hakan yasa suka garzaya wajen fasto don addu’a
- Daga nan ne kuwa fasto ya samu dama don har cikin gida kuma dakin bacci yake biyota don yi mata addu’a inda suke shagalinsu
Abin mamaki baya karewa a duniya. Matar aure ce ke neman shawarar yadda zata tsinke dangantakarta da fasto wanda mijinta ke tsammanin yana zuwa ne don yi mata addu’a. Bai sani ba ashe kwanciya suke a kan gadon aurensu. Matar dai ta ce ta gaji da wannan rayuwar. Tana tunanin sanar da mijinta ne ko kuma ta tona asirin a gaban cocin.
A wani rahoto da Jaridar Gistmania ta wallafa a shafinta na yanar gizo matar tayi magana kamar haka:
“Ina cikin wata babbar matsala da mijina sai ya kai wa fasto koke. Daga nan ne faston ya shigo ciki tare da bani wasu addu’o’in da zan dinga yi na tsawon lokaci. Bayan na kammala ne muka je don kara ganin fasto. A nan yayi mana addu’a sannan ya sallamemu da cewa komai lafiya.
“Bayan makonni biyu ne matsalar ta kara dawowa. Ni da mijina kiyayya me tsanani ta shiga tsakaninmu don mun koma tamkar bera da kare a gidanmu. Faston ya kara gayyatarmu tare da yi mana addu’a a cikin cocin. Bayan ya kammala ne ya ce mijina ya fita ya barmu.
KU KARANTA: Man 'Bleacing' mai tsada muke shafawa shine yasa muka fi dan uwanmu fari - Rahama Sadau ta mayar da martani
“Daga baya sai suka yi yarjejeniya da mijina a kan zai dinga zuwa gidanmu don yi mana addu’a. Sau da yawa ana addu’ar ne a cikin dakin baccinmu yayin da mijina yake waje yana jiranmu. Daga nan kuwa sai fasto ya fara zuwa wajena a lokutan da mijina baya gida.
“Ta kai ga ko mijina yana gida haka muke shiga dakin baccinmu mu gama abinda zamu yi ba tare da ya yi zaton komai ba. Gaskiyar magana ita ce. Ni da fasto muna cin amanar mijina ne yayin da muke addu’ar a daki.
“A halin yanzu hankalina ya ki kwanciya kuma na gaji da abinda muke yi. Na rasa yadda zanyi in dena. In sanar da mijina ne ko kuma in bayyana hakan ne a gaban coci?” cewar matar auren.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng