Wa'iyazubillah: Da idona na kama mahaifina yana wanka da mijina - Matar aure

Wa'iyazubillah: Da idona na kama mahaifina yana wanka da mijina - Matar aure

- A cewarta, watanninsu uku da aure amma bai taba sauke hakkin aure da yake kan shi ba

- Kullum yana manne da mahaifinta don tare suke wanka ko kuma cikin dare ya koma dakin mahaifin nata

Wata mata mai suna Adedolapo ta koka a kafar sada zumunta bayan ta gano mijinta tamkar mijin mahifinta yake. Adedolapo ta koka da yadda mijinta da mahaifinta ke shiga wanka tare amma mijin nata ya kasa sauke hakkin shi na aure a kanta.

Kamar yadda ta ce, “Ni kadai mahaifina ya haifa a duniya kuma nayi aure ne watanni uku da suka gabata. Duk wani gatan aure da shagali anyi min kuma na tare da mijina.

“Mahaifina ne ya hada ni da wanda na aura duk da bansan mijin nawa sosai ba kafin muyi aure. Mahaifina ya ce a wajen aikinsu yake kuma ya ga hotona ne a wayar shi daga nan ya bayyana cewa yana sona. Ban bata lokaci ba na amince shine muka hadu da juna.

“Cikin watanni biyu kadai aka gaggauta aka mana aure. Matsalar ta fara ne lokacin da mahaifina ya dawo gidanmu bayan munyi aure. Abin bai bata min rai ba don zan dinga amfani da damar ina ganin mahaifina. Amma kuma abin mamakin sai na fara ganin mijina da mahaifina suna shiga da fitowa wanka tare.

KU KARANTA: Tashin hankali: Sirika ta nemi mijin 'yarta yayi lalata da ita saboda suyi arziki

“Sau da yawa mijina yana fita daga dakin baccinmu da wurwuri don wankan sassafe da mahaifina amma abin bai fara yin yawa ba sai bayan da muka yi watanni uku da aure. Mijina baya taba ni ko kadan amma kullum yan manne da mahaifina.

“Lokuta da yawa mijina na zuwa dakin mahaifina ya kuma fito yana matukar zufa. Haka da dare yake zuwa wajen mahaifina inda daga baya yake dawowa cikin dare wajena. Nayi kokarin yi wa mijina magana amma ya ce babu abinda ke faruwa. Yanzu da na kara magana sai ya fara fada. Hatta mahaifina baya so a yi maganar, Ina bukatar shawararku don ina kaunar mijina,” cewar matar auren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel