Yadda wani mutum ya yi wa matarsa duka har sai da ta mutu

Yadda wani mutum ya yi wa matarsa duka har sai da ta mutu

'Yan sanda sun kama wani dan shekara 40, Olanrewaju Bamidele a jihar Ogun da aka ce ya yi wa matarsa, Adenike dukan tsiya kuma daga bisani ya caka mata wuka ta mutu.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Janairun 2020 bayan sun samu rashin jituwa a gidansu da ke kauyen Bisodun, Ofada a karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Oyeyemi ya ce dan matar mai shekaru 15, Ayomide ne ya sanar da 'yan sanda cewa mahaifiyarsa ta samu rashin jituwa da mahaifinsa ne kuma hakan ya yi sanadiyar fada tsakannsu.

A cewar kakakin 'yan sandan, Ayomide ya ce mahaifinsa ya yi amfani da babban sanda ya yi wa matarsa duka har ta suma daga bisani kuma ya caka mata screw driver a kai wadda hakan ya yi sanadin mutuwarta.

Oyeyemi ya ce, "Bayan samun rahoton, dan sandan da ke kula da caji ofis na Ofada, DSP Akinfolahan Oluseye ya tafi da mutanensa zuwa kauyen Bisodun inda wanda ake zargin ya ke kuma mutane suka mika shi hannun 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Innalillahi: Dan babban malamin Musulunci a duniya ya mutu sakamakon harbin bindiga

"Daga nan an garzaya da shi zuwa hedkwatan 'yan sanda inda ake masa tambayoyi.

"Binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa wanda ake zargin ya saba dukan matarsa lokaci zuwa lokaci kuma bayan ya yi mata duka ta mutu, ya na kokarin birne ta a kusa da gidansu ne sai yaransa suka ganshi kuma suka sanar da makwabta inda aka rike shi har 'yan sanda suka zo.

"Gawar matar yana asibitin koyarwa na Onabanjo da ke Sagamu domin bincike kuma an gano screw driver da aka yi amfani da shi wurin kashe ta."

Mai magana da yawun 'yan sandan ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandna jihar, Kenneth Ebrimson ya bayar da umurnin a mika binciken zuwa sashin binciken manyan laifuka wato CID don zurfafa binciken.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel