Yadda matar aure da umurci mijinta ya rika kwanciya da mahaifyarta saboda neman abin duniya

Yadda matar aure da umurci mijinta ya rika kwanciya da mahaifyarta saboda neman abin duniya

Wani magidanci dan kasar Zimbabwe ya bawa mutane mamaki bayan ya yi ikirarin cewa matarsa ta bashi izinin ya rika kwanciya da mahaifyarta saboda su samu arziki.

Mutumin, mai suna Manfred Nhemachena ya kuma bayyana cewa surukarsa Beatrice Marabawa ta nemu ya rika kwanciya da ita saboda mijinta baya biya mata bukatunta yayin kwanciya.

Wannan lamari ya fito fili ne a kotun Bulawayo inda tsohuwar matarsa, Tariro Nhemachena ta nemi kotu ta bata kariya domin mijinta yana jin zarafinta kamar yadda B Metro ta ruwaito.

Manfred da Tariro sun yi aure ne a ranar 10 ga watan Afrilun 2010 kuma suna da da guda daya mai shekaru 10 duk da a yanzu basu tare amma ba a katse igiyar auren ba.

Manfred ya ce, "Abin takaici ne da kunya, tun daga lokacin na dena ganin mutuncin ta. Na gode wa Allah ban amince na aikata mummunan abinda ta nemi in aikata ba.

"Na fara lura akwai alamun matsala a lokacin da ta zo hutu gidan mu a 2015. Ban dauki abin da zafi ba har sai lokacin da ta nemi ta fara zuwa daki na ta kwana.

"Da na tambayi dalilin da yasa ta ke son kwana a daki na sai ta ce mijinta (surukina) ya dena biya mata bukatunta yayin kwanciya."

Ganin irin wannan abinda surukarsa ta yi, Manfred ya nemi ta tafi da gana da 'yan uwansa.

Amma wai bata yi ammana da hakan ba inda ta ce za ta tilasta masa kwanciya da ita.

"Da ta fara kwanciya a uwar dakan mu ni kuma sai na kwashe kaya na na koma wani dakin daban.

"Daga bisani sai ta fara sanya kaya masu jan hankali ta biyo ni dakin da na koma ta zauna a cinya ta. Daga ranar ita ke min abinci ta kan kuma goge min tufafi na."

Manfred ya ce hankalinsa ya tashi domin baya kaunar ganin surukarsa cikin irin wannan halin.

Ya kuma ce bayan ya shaidawa matarsa abinda mahaifiyarta ke neman aikatawa, amsar da matarsa ta bashi ya razana ni.

DUBA WANNAN: Innalillahi: Dan babban malamin Musulunci a duniya ya mutu sakamakon harbin bindiga

"Abinda ta ce shi ne, "Eh, ta gaske ne ba su kwanciya tare kuma da kwanta da ita, za mu samu arziki."

Ya kara da cewa, "Rai na ya baci bayan jin hakan a bakinta, daga nan ne na yanke shawarar barin gidan."

Ya ce ya yi kokarin tuntunbar surukinsa da 'yan uwansa amma abin bai yiwu ba.

Sai dai da aka tuntube surukarsa, Beatrice Marabawa ta karyata zargin da Manfred ya yi inda ta ce dama shi tantirin makaryaci ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel