Tashin hankali: Sirika ta nemi mijin 'yarta yayi lalata da ita saboda suyi arziki

Tashin hankali: Sirika ta nemi mijin 'yarta yayi lalata da ita saboda suyi arziki

- Wani mutum dan asalin kasar Zimbabwe ya shiga tashin hankali da rudani saboda bukatar sirikar shi

- Manfred ya ce sirikar shi ta bukaci ya kwanta da ita don zasu samu kudi mai tarin yawa

- Ta tattara ta dawo gidan shi inda take bin duk hanyoyin jawo hankalin shi ta hanyar shiga mai bayyana sura a waje

Wani mutum dan asalin kasar Zimbabwe ya shiga rudani da tashin hankali bayan sirikar shi ta bijiro da bukatarta mai ban mamaki gare shi.

Mutumin mai suna Manfred ya koka da yadda matar shi ta shirya da mahaifiyarta don ta kwanta dashi da burin zasu yi kudi.

Manfred ya bayyana yadda matar shi ta shekaru 10 ta bukaci ya yi lalata da mahaifiyarta don su yi kudi. Kamar yadda Jaridar Drum Beat News ta bayyana.

Manfred ya sanar da hakan ne bayan matar shi mai suna Nhemechena ta maka shi a kotu tare da bukatar alkali ya shiga tsakaninsu don yana cin zarafinta.

A tattunawar da yayi da manema labarai, Manfred ya ce matar shi ta bukaci ya kwanta da mahaifiyarta ne.

Ya ce, "abun kunya ne kuma mutuncinta ya zube a idona. Nayi godiya ga Ubangiji da ban fada tarkonsu ba."

KU KARANTA: Tsananin sanyi ya sanya yanzu bama samun kasuwa - Karuwan jihar Kano sun koka

"Na fara ganota ne tun a 2015 da ta zo zama tare damu. Ta fara bukatar mahaifiyarta ta kwana tare da mu a daki daya amma da na bukaci sanin dalili, sai ta ce mahaifinta baya kwanciya da mahaifiyarta."

Ya ce ya bukaci ya samu sirikin shi don ya sasanta su amma sai taki tare da neman tirsasa shi ta karfi.

"Na bar musu dakin baccinmu inda na koma wani dakin amma sai washegari ta biyo ni bayan tayi shigar banza. Ta tarar ina bacci amma sai ta hau cinyata tare da fara wasa dani. Daga ranar ta koma kawo min abinci tare da yi min hidima. A duk lokacin da nayi dare ita ke bude min kofa sanye da kaya masu nuna jiki.

"A lokacin da na sanar da matata, sai ta ce in kwanta da ita don zamu yi kudi." Manfred ya ce.

Kamar yadda rahoto ya nuna, sun rabu kuma ana tafka shari'a a kan wanda zai rike dan su mai shekaru hudu a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel