Yanzu-yanzu: Kotu koli ta tabbatar da Gwamna Simon Lalong

Yanzu-yanzu: Kotu koli ta tabbatar da Gwamna Simon Lalong

Bayan hutun rabin lokacin kimanin sa'o'i hudu da aka dauka Kotun kolin Najeriya a yau Litinin ga watan Junairu, 2020, alkalai masu shari'a sun tabbatar da Simon Bako Lalong matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Plateau.

Kotun ta raba gardamar ne bayan watanni goma da hukumar gudanar da zabe INEC ta alantashi matsayin zakaran zaben 9 ga Maris, 2020.

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta Jeremiah Useni, sun shigar da kara kotu ne domin kalubalantar nasarar APC a zaben.

Amma Alkalan kotun kolin sun yi ittifakin watsi da karar a shari'ar da Alkali Adamu Galinje, ya karanta.

Mun kawo muku cewa kotun koli ta tabbatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, matsayin gwamnan jihar Kano bayan watsi da karar Abba Kabir Yusuf da PDP.

Hakazalika kotun ta yi watsi da karar Ahmad Aliyu Sokoto da jam'iyyar APC inda suka kalubalanci nasarar gwamna Aminu Waziri Tambuwal a jihar Sokoto.

Duk a yau, Shugaban alkalan Najeriya, Justis Tanko Muhammed bai halarci zama ba a lokacin da kotun koli ta fara yanke hukuncinta kan karar da aka daukaka kan zaben gwamnan jihar Kano.

A madadinsa, Justis Sylvester Ngwuta ke jagorantar kwamitin alkalan mai dauke da mambobi biyar.

Sauran sun hada dan Justis Kudirat Kekekere-Ekun, Justis Olukayode Ariwoola, Justis Amina Augie da kuma Justis Uwani Abba-Aji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel