Rundunar sojoji ta gargadi hukumomin kasashen ketare a goyon bayan Boko Haram

Rundunar sojoji ta gargadi hukumomin kasashen ketare a goyon bayan Boko Haram

A ranar Litinin ne rundunar sojin Najeriya ta ja kunnen kasashen ketare a kan shiga lamurran da suka shafi tsaron kasar nan ballantana yaki da Boko Harama da kuma ISWAP.

Duk da rundunar sojin ba ta sanar da sunayen cibiyoyin ba, ta shawarci cibiyoyin gida da na wajen da su kiyaye wajen goyon bayan kungiyoyin ta’addancin.

Amma kuma ta jaddada cewa ana ci gaba da yakar ta’addancin da ya yi katutu a yankin Arewa maso gabas, ko kuma sauran bangarorin kasar nan.

Kamar yadda takardar da shugaban yada labarai na rundunar sojin, Col. Aminu Iliyasu yasa hannu, “Shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ana cigaba da fada da makiyan kasar nan masu hana zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas na kasar nan.

DUBA WANNAN: Kotun koli: Murna ta barke a kan nasarar Ganduje a Kano

“Bayan dogon nazari a kan ayyukan sojin a Arewa maso gabas, za a iya ganin cewa hedkwatar rundunar sojin ta shirya tsaf don shawo kan matsalar tsaron tare da tabbatar da kafuwar Najeriya mai cike da zaman lafiya ba tare da ta'addanci ba.”

“Shugaban rundunar sojin Najeriya ya ja kunnen makiyan Najeriya da ‘yan Najeriya masu jin dadin tashin-tashinar cewa akwai ranar sakamako. Duk wasu ‘yan najeriya da kuma masu ruwa da tsaki ana jawo hankulansu da su goyi bayan yaki da rashin zaman lafiyar a kasar nan.” In ji Buratai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel