Sakamakon shari'ar kotun koli: An barke da murna da shewa a jihar Sokoto

Sakamakon shari'ar kotun koli: An barke da murna da shewa a jihar Sokoto

Yan jam'iyyar People Democratic Party (PDP) da masoya gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, sun barke da murna da shewa a jihar Sokoto bayan kotun koli ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar.

Mutan jihar sun fito kwansu da kwarkwatansu domin nuna farin cikinsu kan nasarar da gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samu a kotun koli.

Duk da cewa cibiyar daular Islamiyyar na cikin lumana gabanin shari'ar kotun, yawancin yara da dalibai sun ki zuwa makaranta yau Litinin bisa ga tsoro abin da ka iya biyo bayan shari'ar.

A unguwar Mabera, matasa sun yi cincirindo suna wakokin murnan "Sai Matawalle, Sai Matawalle".

Yayinda wasu ke rike da tutar PDP, wasu na rike da hotunan gwamnan suna murnan nasara.

Amma da jami'an tsaro sun bazama cikin garin domin tabbatar da tsaro da gudun barkewar rikici tsakanin yan jam'iyyar hamayya.

Daya daga cikin masu murnar ya bayyanawa Daily Trust cewa : "Yau ya kawo karshen shari'ar gaba daya. Muna murna da mika godiya ga Allah."

Mun kawo muku cewa kotun koli ta tabbatar da Aminu Waziri Tambuwal matsayin gwamnan jihar Sokoto.

Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki wajen watsi da karar jam'iyyar All Progressives COngress APC da dan takararta, Ahmad Aliyu Sokoto.

Za ku tuna cewa a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2019, jam'iyyar APC a jihar Sokoto ta lashi takobin garzayawa kotun koli bayan kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na jadada nasarar Gwamna Aminu Tambuwal.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel