Kotun koli: Murna ta barke a kan nasarar Ganduje a Kano

Kotun koli: Murna ta barke a kan nasarar Ganduje a Kano

Garin Kano a ranar Litinin ya cika da murna tare da farin ciki bayan kotun koli ta jaddada nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zaben ranar 9 ga watan Maris 2019.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa miliyoyin jama'ar jihar sun fito daga gidajensu don nuna murnarsu bisa ga nasarar Ganduje duk da sanyin da garin ke ciki.

A hankali kuwa jama'a suke komawa kan harkokinsu na yau da kullum a fadain jihar.

A yayin martani ga nasarar Ganduje, Kwamishinan yada labarai da al'adu na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya ce ikon Allah ne da kuma burin mutane suka tabbata.

DUBA WANNAN: Ganduje da Tambuwal: 'An kasa tsaye, an kasa zaune' a Kano da Sokoto saboda jiran hukuncin koli a yau

Kamar yadda ya ce: "Muna matukar godiya ga Allah a kan wannan nasarar. Wannan nasarar ba ta Ganduje ba ce shi kadai, nasarar jama'ar jihar Kano ce baki daya.

"Muna kira ga jam'iyyar PDP da su kwantar da hankalinsu tare da rungumar hukuncin da hannu bibbiyu. Wannan tabbaci ne na tafiyar mu zuwa mataki na gaba".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel