Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun jikkata yayinda wata babbar mota dauke da yan PDP da ke zanga-zanga a Abuja ta fadi

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun jikkata yayinda wata babbar mota dauke da yan PDP da ke zanga-zanga a Abuja ta fadi

- Wata babbar mota da ke dauke da mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke gudanar da zanga-zanga a Abuja ta mirgina kasa

- Mutane da dama sun jikkata yayin afkuwar lamarin wanda ya wakana a mararrabar Transcorp Hilton

- Suna zanga-zangar ne domin nuna rashin amincewarsu da hukuncin kotun na ranar Talata da ta gabata inda ta tsige Emeka Ihedioha a matsayin gwamnan jihar Imo

Wani abun bakin cikin ya afku a ranar Litinin, 20 ga watan Janairu a lokacin zanga-zangar da mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke gudanarwa a Abuja inda wata babbar mota da ke sauke dasu zuwa wajen taron ta fadi, inda wasu da dama daga cikinsu suka jikkata.

Lamarin ya afku ne a mararrabar Transcorp Hilton lokacin da direban motar ya juya yayinda magoya bayan jam’iyyar ke a hanyarsu ta zuwa harabar kotun koli domin nuna rashin amincewarsu da hukuncin kotun na ranar Talata da ta gabata inda ta tsige Emeka Ihedioha a matsayin gwamnan jihar Imo.

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun jikkata yayinda wata babbar mota dauke da yan PDP da ke zanga-zanga a Abuja ta fadi
Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun jikkata yayinda wata babbar mota dauke da yan PDP da ke zanga-zanga a Abuja ta fadi
Asali: UGC

Da farko dai Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fara zanga-zangarta da ta shirya a Abuja a safiyar ranar Litinin, 20 ga watan Janairu.

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun jikkata yayinda wata babbar mota dauke da yan PDP da ke zanga-zanga a Abuja ta fadi
Mutane da dama sun jikkata yayinda wata babbar mota dauke da yan PDP da ke zanga-zanga a Abuja ta fadi
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kotun koli ta tabbatar Bala Mohammed matsayin gwamnan Bauchi

Shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, da wasu manyan mambobin jam’iyyar na daga cikin mutanen da ke gagarumin zanga-zangar wanda ke gudana a yanzu haka.

Babbar jam’iyyar adawa a wani jawabi da ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce ya zama dole kotun koli ta janye hukuncinta kan zaben gwamnan jihar Imo wanda ya sallami dan takararta, Emeka Ihedioha, sannan ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Hope Uzodinma a matsayin sahihin zababben gwamnan jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel