Tun lokacin da Zulum ya tsawatawa Sojoji masu karban na goro suka daina tsaronmu - Mazauna

Tun lokacin da Zulum ya tsawatawa Sojoji masu karban na goro suka daina tsaronmu - Mazauna

Mazauna kauyukan dake kan titin Damaturu zuwa Maiduguri sun bayyana cewa yan Boko Haram na kawo musu hari kulli yaumin amma jami'an Sojojin Najeriya sun daina basu tsaro, Rahoton The Cable.

Mazaunan da suka tattauna da manema labarai sun bayyana cewa Soji sun yi batan dabo ne tun lokacin da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya tuhumci Sojojin da karban na goro daga hannun matafiya.

Zaku tuna cewa gwamna Zulum ya zajjara Sojoji kan zaluntar matafiya.

Wani mazaunin da aka sakaye sunansa yace: "Tun ranar da gwamna ya yiwa Sojoji ihu, kamar dukkansu sun tafi. Tun daga ranar ake kaiwa kauyukanmu hari kulli yaumin."

"Ana garkuwa da matafiya kowani lokaci kuma Sojoji sun cire sansaninsu, maharan na cin karansu ba tare Soji sun tsayar da su ba."

Wani mazaunin yace yan kauyukan sun arce zuwa Maiduguri yayinda saura suka gudu Damaturu.

"Yan kauyen Auno, Jakana da Benishek suna arcewa daga muhallansu zuwa Maiduguri. Yan ta'addan sun kai hari akalla sau biyu kauyukan,"

"Kuma abin takaicin shine babu gwamna kadai ne ke magana. Dattawan Borno basu magana, NSA, shugaban NNPC, shugaban EFCC, dukka yan Borno ne kuma babu wanda yayi magana cikinsu kan titin Damaturu zuwa Maiduguri."

Za ku tuna cewa Kakakin hukumar Soji ya bayyana cewa iwun da gwamna Zulum ya yiwa Sojoji kan amsan na goro na iya kawo cikas cikin yakin Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel