YANZU-YANZU: Kotu ta tabbatar da Tambuwal matsayin gwamnan jihar Sokoto

YANZU-YANZU: Kotu ta tabbatar da Tambuwal matsayin gwamnan jihar Sokoto

Kamar yadda tayi kan karar jihar Kano, kotun koli ta tabbatar da Aminu Waziri Tambuwal matsayin gwamnan jihar Sokoto.

Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki wajen watsi da karar jam'iyyar All Progressives COngress APC da dan takararta, Ahmad Aliyu Sokoto.

Za ku tuna cewa a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2019, jam'iyyar APC a jihar Sokoto ta lashi takobin garzayawa kotun koli bayan kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na jadada nasarar Gwamna Aminu Tambuwal.

A yayin zantawa da ya yi da manema labarai jim kadan bayan yanke hukuncin, Barrista Bashir Jodi wanda ya yi magana a madadin lauyoyin jam'iyyar ya ce jam'iyyar tana da kwararran dalilai da yasa za ta daukaka kara a kan hukuncin.

A bangare guda, Shugaban alkalan Najeriya, Justis Tanko Muhammed bai halarci zama ba a lokacin da kotun koli ta fara yanke hukuncinta kan karar da aka daukaka kan zaben gwamnan jihar Kano.

A madadinsa, Justis Sylvester Ngwuta ke jagorantar kwamitin alkalan mai dauke da mambobi biyar.

Sauran sun hada dan Justis Kudirat Kekekere-Ekun, Justis Olukayode Ariwoola, Justis Amina Augie da kuma Justis Uwani Abba-Aji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel