Zulumi: Gwamnan Bauchi ya isa kotun koli da tawagarsa

Zulumi: Gwamnan Bauchi ya isa kotun koli da tawagarsa

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed na daga cikin manyan baki a kotun koli a yau da za a yanke hukuncin karshe a kan zaben kujerar gwamnan jihar da aka yi a ranar 9 ga watan Maris.

A makon da ya gabata, gwamnan bai samu halartar zaman kotun ba saboda yana kwance a gadon asibiti a London, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rade-radin cewa yana kwance a gadon asibiti a London yasa gwamnatin jihar ta musanta rahoton da ake yadawa na cewa Bala Muhammed ba zai dawo nan kusa ba don cigaba da sauke nauyinsa na mulkin jihar.

DUBA WANNAN: Ganduje da Tambuwal: 'An kasa tsaye, an kasa zaune' a Kano da Sokoto saboda jiran hukuncin koli a yau

A wata takarda da babban mataimakinsa na musamman a kan yada labarai, Mukhtar Gidado yasa hannu, ya ce "wasu daga cikin 'yan adawa na murnar cewa halin rashin lafiyar gwamnan na ta'azzara a yayin da ake shari'a a kotun koli."

Idan an lura za a gane cewa wasu 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki a jihar Bauchi sun kasa zaune ko tsaye sakamakon jira hukuncin karshe na zaben gwamnan jihar da za a bayyana a yau Litinin.

Amma kuma, kungiyar dattijan jihar Bauchi mai tabbatar da zaman lafiya da mulki nagari tayi kira ga 'yan jihar da su karba duk hukuncin da ya fito daga kotun kolin da hannu bibbiyu tare da imani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel