Dundum! Boko Haram ta lalata wutar lantarkin garin Maiduguri

Dundum! Boko Haram ta lalata wutar lantarkin garin Maiduguri

Matsalar wutar lantarki na cigaba da ta’azzara a garin Maiduguri da kewaye na jahar Borno sakamakon hare haren da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai ma kayan aikin dakon wutar lantarki wuta, wanda hakan ya jefa garin cikin duhu tun ranar Juma’a.

Daily Trust ta ruwaito manajan watsa labaru na hukumar dakon wutar lantarkin Najeriya, TCN, Ndidi Mbah ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 19 ga watan Janairu inda yace yan ta’addan sun lalata wayoyin lantarkin dake tsakanin Maiduguri da Damaturu.

KU KARANTA: Ramin Kura: Ministar Najeriya ta nada diyar cikinta wani babban mukami a ofishinta

TCN ta bayyana cewa injiniyoyinta sun gano matsalar a tsakanin Maiduguri da Damaturu, kuma zasu fara aikin gyaransa nan bada jimawa ba. “Zamu mayar da wutar lantarki garin Maiduguri zuwa ranar Litinin. Muna kara yaba ma kokarin jami’an Sojan Najeriya bisa kokarin da suke yi wajen kare kayan aikinmu.”

Daga karshe hukumar ta bayyana damuwarta gami da rashin jin dadinta bisa matsanancin halin rashin wutar lantarki da wadannan hare hare suka jefa garin Maiduguri da ma wasu sassan jahar Borno a ciiki.

A wani labarin kuma, Rundunar sojin 1 Div sun damke wani mutumi dan shekara 50 mai suna, Ahmadu Mohammed, wanda ake zargi da safarar makamai kuma an samu bindigogi 10 a hannunsa. Daily Trust ta ruwaito.

Majiya daga gidan soja ta bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a ranar Lahadi a Kaduna cewa an damke mai safarar bindigan ne misalin karfe 12:30 na ranar Juma'a.

Majiyar ta ce an damke mutumin yayinda ya nufi Pandogari, jihar Neja domin kaiwa wani shahrarren dan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Yunusa Madaki, bindigogin. Majiyar ta kara da cewa Ahmadu ya kasance mai kaiwa yan bindiga da masu garkuwa da mutane bindiga da suka amfani da shi wajen addaban mutane a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel