Ziyarar Landan: Shugaba Buhari ya gana da babban Dan Sarauniyar Ingila, yarima Charles

Ziyarar Landan: Shugaba Buhari ya gana da babban Dan Sarauniyar Ingila, yarima Charles

A yayin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai kasar Birtaniya, ya samu ganawa da wani babban jami’I a fadar Sarauniyar Ingila, kuma babban dan Sarauniya Elizabeth, watau Yarima Charles, mai jiran gado.

Shugaban kasa Buhari ne da kansa ya yi tattaki zuwa gidan Yarima Charles dake birnin Glasgow a kasar Scotland, kuma ya samu rakiyar manyan hadimansa da wasu manyan jami’an gwamnati dake aiki a ofishin jakadancin Najeriya a Ingila.

KU KARANTA: Ramin Kura: Ministar Najeriya ta nada diyar cikinta wani babban mukami a ofishinta

Ziyarar Landan: Shugaba Buhari ya gana da babban Dan Sarauniyar Ingila, yarima Charles
Buhari da Charles
Asali: Facebook

Idan za’a tuna Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi birnin Landan na kasar Birtaniya ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Janairu domin halartar taron zuba jari tsakanin kasar Birtaniya da kasashen nahiyar Afirka da za’a yi a ranar Litinin, 20 ga watan Janairu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, inda yace firai ministan kasar Birtaniya, Boris Johnson ne ya shirya taron, kuma shi ne babban mai masaukin baki.

Mashirya taron sun bayyana cewa suna fatan taron zai hada gamayyar shuwagabannin kasashen Afirka, shuwagabannin kamfanoni masu zuba jari da kuma shuwagabannin hukumomi da kungiyoyi domin hada hannu wajen zuba jari da samar da ayyuka domin amfanin jama’an Afirka da Birtaniya.

Ziyarar Landan: Shugaba Buhari ya gana da babban Dan Sarauniyar Ingila, yarima Charles
Buhari da Charles
Asali: Facebook

“Baya ga tattauna sabbin bangarorin hadin gwiwa da zasu kawo cigaba tsakanin Birtaniya da Afirka, za’a kuma a tattauna batun kudi da manyan ayyuka, ciniki da kasuwanci, matsalolin yanayi da kuma yadda cigaban Afirka zai kasance a nan gaba.

“Taron zai baiwa Najeriya daman gabatar da kanta ga duniya a matsayin kasar da ta fi cancanta su zuba jari a cikinta. Haka zalika taron zai zurfafa alakar cinikayya tsakanin Najeriya da Birtaniya, musamman duba da yiwuwar Birtaniya daga kungiyar tarayyar turai.” Inji Adesina.

Ziyarar Landan: Shugaba Buhari ya gana da babban Dan Sarauniyar Ingila, yarima Charles
Buhari da Charles
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda zasu raka Buhari akwai gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello, gwamnan jahar Gombe, Muhammad Inuwa da kuma gwamnan jahar Abia, Okezie Ikpeazu, sai kuma ministar kudi Zainab Ahmad, ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama da ministan cinikayya da kasuwanci, Niyi Adebayo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel