An damke wnai mai sayarwa yan bindiga makamai a Kaduna

An damke wnai mai sayarwa yan bindiga makamai a Kaduna

Rundunar sojin 1 Div sun damke wani mutumi dan shekara 50 mai suna, Ahmadu Mohammed, wanda ake zargi da safarar makamai kuma an samu bindigogi 10 a hannunsa. Daily Trust ta ruwaito.

Majiya daga gidan soja ta bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a ranar Lahadi a Kaduna cewa an damke mai safarar bindigan ne misalin karfe 12:30 na ranar Juma'a.

Majiyar ta ce an damke mutumin yayinda ya nufi Pandogari, jihar Neja domin kaiwa wani shahrarren dan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Yunusa Madaki, bindigogin.

Majiyar ta kara da cewa Ahmadu ya kasance mai kaiwa yan bindiga da masu garkuwa da mutane bindiga da suka amfani da shi wajen addaban mutane a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

A cewar Majiyar: "Bisa ga labarin leken asiri mai inganci, Sojoji sun damke motar da ke dauke da mai safarar bindigan."

"Bayan binciken da aka gudanar cikin motar, an samu bindigogi 10 masu amfani da harsasan 7.62mm."

"An boye bindigogin cikin buhun bawon wake."

"Yayinda aka yi masa tambayoyi, mutumin ya bayyana cewa wani mai hada bindigogi Ali Makeri ne ya aikeshi kaiwaa Yunusa Madaki, mazaunin kauyen Shamuyabo dake Pandogari, bindigogi."

"Madaki shahrarren dan bindiga ne wanda ke cikin kerin wadanda ake nema ruwa a jallo."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel