An datse wa wani almajiri kai a Beji

An datse wa wani almajiri kai a Beji

Wasu wadanda har yanuz ba a san ko su waye ba sun cire wa almajiri kai a Beji dake Minna a jihar Neja. Har yanzu dai ba a gano dalilin hakan ba amma za a iya danganta hakan da tsafi.

Asalin almajiri dai mai neman ilimi ne ba mabaraci ba. Yawan da suke yi a makarantunsu kuma da halin ko-in-kula da iyayensu ke nuna musu ta yadda basu waiwayarsu a makarantunsu ke sa su koma bara.

Amma kuma suna gamuwa da illoli daban-daban a rayuwarsu a yayin da suek yawo lungu-lungu a tituna. Illolin sun hada dana lafiyar jikinsu da kuma yadda suke cin karo da bata-gari marasa imani.

Wannan lamarin na da matukar ban haushi da tada hankali.

Amma kuma wani salon cih zarafi da ake wa yaran bayan cin zarafin yasar dasu da iyayensu suke yi, Malaman makarantun kan tura su bara don nemo wa gidan malamin abinci da kudi don amfanin kansa.

DUBA WANNAN: Mahaifin Sulaiman ya gindaya wa Ba Amurkiyar data zo auren dansa sharudda guda 4

A maimakon a bar yaron ya ji da matsalolin rayuwarsa, a kan kara masa da wani nauyi da yafi karfinsa.

Hakazalika, wasu malaman kan bada hayar daliban don aiki a gonar mutane ko kuma gonar malamin alokacin damina ko kuma lokacin girbin amfanin gona.

Wannan tsananin rashin gatan ne ke sa ana cin zarafin yaran ta hanyar tozarta su ko kuma rasa rayukan wasu daga ciki dungurungun.

Muna fatan Iyaye su dau wannan ya zama darasi garesu kuma Allah ya gafartawa wannan Almajiri da ya rasa ransa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel