Kungiyar yan ta'addan Ansaru ta dau alhakin harin da aka kaiwa Sarkin Potiskum

Kungiyar yan ta'addan Ansaru ta dau alhakin harin da aka kaiwa Sarkin Potiskum

Kungiyar yan ta'adda a Sudan, Jama'atu Ansarul Muslimeen, ta dau alhakin harin da aka kaiwa mai martaba sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram, a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Shahrarren lauya, Audu Bulama Bukarti, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita inda ya bayyana cewa wannan alama ne na kungiyar Ansaru na kokarin dawowa bayan murkusheta tun shekarar 2012.

Harin karshe da yan ta'addan Ansaru suka kai shine garkuwa da turawa bakwai a kamfanin Setraco a jihar Kano a watan Febrairu 2013.

Bulama ya ce yan kungiyar sun dau alhakin harin ne a tashar yada labaran Al-Qa'ida, Thabat.

Wannan shine karo na farko tun shekarar 2013 da zasu dau alhakin kai wani hari.

Akalla mutane 30 suka rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da 100 lokacin da yan bindiga suka budewa motoci wuta a babbar titin Kaduna zuwa Zariya ranar 14 ga watan Junairu, 2020.

Hukumar yan sandan jihar, a jawabin da ta saki ta bayyana cewa yan bindigan sanye da kayan Sojoji sun kai harin ne misalin karfe 11 na dare.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya ce mutane shida kadai aka kashe kuma biyar sun jikkata. Ya tabbatar da cewa an yi awon da wasu amma bai bayyana adadinsu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel