Fusatattun matasa sun banka wa hedikwatar PDP wuta

Fusatattun matasa sun banka wa hedikwatar PDP wuta

An banka wa ofishin jam'iyyar PDP na karamar hukumar Nsukka dake jihar Enugu wuta. Wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka yi wannan aika-aikar.

An gano cewa kona ofishin na karamar hukumar Nsukka din bashi da hadi da yakin neman zaben karamar hukumar dake gabatowa a jihar.

Shugaban jam'iyyar a karamar hukumar Nsukka, Fabian Onah ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a Nsukka.

Ya ce an kira shi ne sassafen ranar da abin ya faru inda aka bayyana masa cewa an banka wa ofishin wuta.

"A lokacin da na samu kira, a take na garzaya ofishin jam'iyyar don gani da idona irin barnar da aka yi mana. Anyi nufin kona ofishina ne kadai don komai da ke ciki sai da ya kurmushe.

DUBA WANNAN: Buhari ya zayyana alheran rufe bodar Najeriya a Landan

"Dukkan tebura , kujeru, takardu da sauran kayayyakin ofishin duk sun kone,"

Shugaban jam'iyyar a karamar hukumar ya bayyana cewa wasu bata-gari sun haura ofishin jam'iyyar tare da balle tagogi. Sun watsa fetur tare da banka wa ofishin wuta.

"Ban san dalilin kona wannan ofishin ba. Sauran sassan ofishin duk gobarar bata taba ba saboda ofishina suka yi nufin konawa inda akwai muhimman takardu," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel