Gwamnan Sokoto: PDP da APC sun nuna karfin gwiwar samun nasara a kotun koli

Gwamnan Sokoto: PDP da APC sun nuna karfin gwiwar samun nasara a kotun koli

Jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da ta All Progressives Congress (APC) a jihar Sokoto sun nuna tabbacin zama masu nasara yayinda kotun koli za ta zartar da hukunci kan shari’an zaben gwamna wanda dan takarar APC, Ahmed Aliyu ya shigar kan Gwamna Aminu Tambuwal a gobe Litinin, 20 ga watan Janairu.

Sakataren jam’iyyar PDP a jihar, Kabiru Aliyu ya ce: “muna da tabbacin cewa mune zamu yi nasara a dukka abubuwan da ke kewaye da shari’an saboda babu abunda zai canja.

“Alkalan Za su tabbatar da hukuncin mutane da kananan kotuna.”

Sakataren APC a jihar, Sambo Bello Danchadi ya ce: “muna sa ran yin nasara amma mun san lamarin a hannun Allah yake. Muna da yakinin nasara sosai, da ikon Allah za mu yi nasara.”

KU KARANTA KUMA: Imo: Yadda kotun koli ta dumbuzawa Hope Uzodinma kuri’u - YIAGA

A halin da ake ciki magoya bayan gwamnan jihar Sokoto watau Aminu Waziri Tambuwal, da na Abokin hamayyarsa Ahmed Aliyu sun shiga faman addu’o’i saboda shari’ar zaben gwamnan jihar.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa haka wannan yanayi ya ke a jihar Kano, inda Magoya bayan Abdullahi Umar Ganduje su ke ta addu’a domin ganin kotun koli ta ba APC gaskiya a shari’a.

A farkon makon nan ne ake sa ran Alkalan babban kotun Najeriya za su bayyana wanda ya ke da gaskiya a karar shari’a zaben gwamnan jihar Kano da Sokoto da aka yi a farkon shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel