Gayu da kwalisa: Hotuna 6 na kuruciyar Buhari da suka jawo cece-kuce a dandalin sada zumunta
Muhammadu Buhari dan siyasa ne kuma shugaban kasar Najeriya. Sai da ya kai matakin manjo janar kafin yayi ritaya a rundunar sojin Najeriya. Ya taba mulkar Najeriya zamanin mulkin soji daga 1983 zuwa 1985.

Asali: Twitter
Kafin nasararsa a 2015, ya yi takarar shugabancin kasa har sau uku amma bai yi nasara ba. Wannan kuwa bai hana shi fitowa takara a 2015 ba inda yayi nasara karkashin jam'iyyar APC.

Asali: Facebook
Sanannen abu ne idan aka ce Shugaba Buhari mutum ne mai nagarta, kuma mutumin talakawa. Ya shiga rundunar sojin Najeriya ne a 1963 kuma tun daga nan bai dena fafutuka don ganin daidaituwar Najeriya ba.

Asali: Twitter
Mutane da yawa sun kallon shugaban kasar a matsayin wanda bai san gayu da kwalisa ba saboda ko yaushe ana ganinsa da babbar riga ko kaftan. Ba kowa ya san cewa shugaban kasar tsohon dan gayu bane mai cike da kwalisa a zamanin samartakarsa.

Asali: Twitter
Duk da ko a halin yanzu idan ka duba shugaban kasar, zaka gane cewa tabbas dan kwalisa ne.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng