Mazauna kauyen da aka kaiwa Sarkin Potiskum hari sun shiga fargaba

Mazauna kauyen da aka kaiwa Sarkin Potiskum hari sun shiga fargaba

Mazuna kauyen Fandisho dake hanyar Kaduna zuwa Zariya inda aka kaiwa sarkin Potiskum hari a makon nan sun gudu daga muhallansu.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa yawancin mazaunan, musamman mata da yara, sun daina kwana a gidajensu gudun abinda ka iya biyowa baya.

Manema labaran da suka kai ziyara kauyen sun bayyana cewa dukkan wadanda suka gudu daga muhallansu har yanzu basu dawo ba.

Hakazalika mun smau rahoton cewa Sojoji sun dira kauyen a daren Alhams inda suke bi gida-gida sun bincike.

Wani mazaunin garin da aka sakaye sunansa ya ce: "Matanmu da yaranmu sun bar gida tun lokacin da harin ya faru."

"Mun kasance cikin tsoro tun jiya (Alhamis) da Sojoji suka fara gudanar da bincike gida-gida. Sun ce sun zo gani ne ko munada makamai."

Mun kawo muku rahoton cewa Akalla mutane 30 suka rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da 100 lokacin da yan bindiga suka budewa motoci wuta a babbar titin Kaduna zuwa Zariya a ranar Talata, 15 ga Junairu, 2020.

Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya a harin.

Hukumar yan sandan jihar, a jawabin da ta saki ta bayyana cewa yan bindigan sanye da kayan Sojoji sun kai harin ne misalin karfe 11 na dare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel