An karrama shugabanni Musulmai guda 5 da suka 'taka rawar gani' a shekarar 2019

An karrama shugabanni Musulmai guda 5 da suka 'taka rawar gani' a shekarar 2019

'Muslim News Nigeria', Wata jarida mai wallafa rahotanni da labarai da suka shafi harkokin addinin Islama, ta fitar da jerin wasu shugabanni Musulmai guda biyar da ta ce sun taka muhimmiyar rawa a bangaren nuna halayen shugabanci da jagoranci nagari.

A cikin wata mujalla da ta fitar a cikin watan Janairu, 2020, jaridar ta bayyana gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umar Zulum, a matsayin babban gwarzonta na shekarar 2019.

Jaridar ta karrama gwamna Zulum da kuma ministan sadarwa na kasa, Dakta Isa Ali Pantami, wanda ta saka a mataki na biyu bayan Farfesa Zulum.

A cewar jaridar, shugabannin da jagororin sun kasance wakilan addinin Islama, kuma Musulunci yana matukar alfahari da irin kwazon da suka nuna a wuraren aikinsu.

An karrama shugabanni Musulmai guda 5 da suka 'taka rawar gani' a shekarar 2019
An karrama shugabanni Musulmai guda 5 da suka 'taka rawar gani' a shekarar 2019
Asali: Twitter

Ga jerin shugabanni da jagorori biyar a Najeriya da jaridar ta karrama:-

1. Farfesa Babagana Zulum (Gwamnan jihar Borno)

2. Dakta Sheikh Isa Ali Pantami (Ministan sadarwa)

DUBA WANNAN: Buhari ya saka baki a kan hukuncin kisa da Saudiyya ta zartar a kan Malamin Islama dan Najeriya

3. Farfesa Is-shaq Oloyede (Babban rijistara na hukumar tsara jarrabawar shiga makarantun gaba da Sakandire, watau JAMB )

4. Farfesa Lakin Akintola (Darektan kungiyar MURIC mai rajin kare hakkin Musulmi da kuma tabbatar da shugabanci nagari a kasa)

5. Farfesa Fatima Batul Mukhtar (Shugabar jami'ar gwamnatin tarayya dake Dutse, babban birnin jihar Jigawa)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel