PDP ta bayyana jihohin arewa 3 da fadar shugaban kasa ke son kotu ta kwace ta bawa APC

PDP ta bayyana jihohin arewa 3 da fadar shugaban kasa ke son kotu ta kwace ta bawa APC

Shugaban jam'iyyar PDP ta kasa, Uche Secondus ya zargi fadar shugaban kasa da matsa wa kotun koli da ta kwace kujerun gwamnonin jihohin Sokoto, Bauchi, Adamawa da Binuwai a hukuncin da zata yanke a ranar Litinin mai zuwa.

Dukkan jihohi hudun INEC ta bayyana cewa PDP ce ta lashe zabukan da aka yi a ranar 9 ga watan Maris na gwamnonin jihar.

Kotun kolin ta saka ranar Litinin mai zuwa a matsayin ranar da za a bayyana hukuncin daukaka kara dake kalubalantar nasarar wasu jihohi a zaben ranar 9 ga watan Maris.

A yayin jawabi a taron jam'iyyar karo na 87 a Abuja, Secondus yayi kira ga alkalan kotun kolin da kada su maimaita irin hukuncin da suka yi a jihar Imo.

A ranar Talata ne kotun kolin ta kwace kujerar Emeka Ihedioha a matsayin gwamnan jihar Imo, kuma ta bukaci INEC da ta ba Hope Uzodinma takardar shaidar zama gwamnan jihar.

Secondus ya kwatanta wannan hukuncin da damfara, tare da kiran alkalan da suyi adalci.

DUBA WANNAN: Basirar 'yan Najeriya: Matashi ya kirkiri injin bayar da wutar lantarki mai amfani da ruwa, ba fetur ba

"Shugabannin jam'iyyar APC da gwamnatin tarayya na hada kai da INEC tare da wasu cibiyoyin tsaro da suka hada da sojin Najeriya wajen sauya sakamakon zabe," Secondus yace.

"Kwamitin jiga-jigan jam'iyyar na da bayanan sirri ta yadda fadar shugaban kasa da shugabancin jam'iyyar APC ke yi na kokarin kwace jihohin Sokoto, Binuwau, Bauchi da Adamawa tare da barin Kano wacce mu muka ci.

"Mun roki alkalai bakwai na kotun kolin da suka taka rawar gani wajen shari'ar damfarar, da su tseratar da kansu daga sauran shari'un." Cewar Secondus.

Ya zargi fadar shugaban kasar ta bar ayyukanta wadanda ya dace ta shawo kai amma ta mayar da hankali wajen waskar da shugabanci, Secondus ya zarga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel