Ku dena kiran mu NEPA idan kuna son wutan lantarki - DisCos

Ku dena kiran mu NEPA idan kuna son wutan lantarki - DisCos

Sunday Oduntan, Babban direkta na sashin bincike da wayar da kan mutane na kungiyar masu rarraba wutan lantarki ta Najeriya (ANED) ya bukaci 'yan Najeriya su dena kiran mambobinsu NEPA.

ANED wani sashi ne ta kungiyoyin rarraba wutan lantarki ta Najeriya da ake kira (DisCos).

Da ya ke magana a wani shirin talabijin na TVC, ya ce idan 'yan Najeriya suka cigaba da kiransu NEPA, hakan na nufin ba su son wutan lantarki.

National Electric Power Authority (NEPA) ce kamfanin da ke samar da lantarki da rarraba ta a Najeriya kafin daga baya aka canja mata suna zuwa Power Holding Company of Nigeria (PHCN).

Oduntan ya ce: "Na san yadda 'yan Najeriya ke ji idan an zo batun biyan kudi. Amma muna son su fahimci wani abu. Na farko, su dena kiran mu NEPA."

"Sunan mu DisCos, amma fa ba rawan DisCos mu ke yi ba. Mu kamfanoni ne masu rarraba wuta. PHCN ta mutu. NEPA ma ta mutu."

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Na yi tafiya a kafa na sa'o'i biyu bayan harin Boko Haram - Sarkin Potiskum

Da ya ke magana a kan shirin karin kudin wutan lantarkin da hukumar kula da wutan lantarki ta Najeriya (NERC) ke shirin yi, Oduntan ya ce wasu abubuwa ne suka janyo bukatar hakan.

Ya ce, "Fiye da kashi 90 cikin 100 na kayayyakin da muke amfani da su daga kasar waje ake shigo da su."

"Saboda haka dole ayi la'akari da yadda kudi ke hauhawa da sauka da canjin kudin. Ya kamata a lura da kudin da ake kashewa wurin samar da wuta da kudin gas. Idan farashin wadannan abubuwan suka sauka, kudin wuta shima zai sauka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel