Gwamnoni 6 sun halarci daurin auren dan gidan kakakin Buhari, Garba Shehu
Akalla gwamnoni shida sun halarci daurin auren 'dan Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Buhari, Muhammad Garba Shehu da Zuwaira Umar Faruk, da aka daura a Masallacin Annur dake unguwar Wuse, Abuja.
Daga cikin wadanda suka halarci taron sune shugaban kasa, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustaoha; ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi da sakataren din-din-din fadar shugaban kasa, Jalal Arabi.
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne wakilin ango kuma ya amshi auren Zuwaira a madadin Malam Garba Shehu.
Sauran gwamnonin da suka halarci daurin auren sune gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru; gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong.
Sauran sune gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu; da gwamnan Edo, Godwin Obaseki.
Shugaba Buhari da uwargidarsa, Aisha, sun aika wasikar taya murna zuwa da Garba Shehu.

Asali: Facebook
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng